13 Janairu 2021 - 13:38
Uganda Ta Bada Umarnin Dakatar Da Shafukan Sada Zumunta

Hukumomi a Uganda sun bukaci kamfanonin dilancin intanet a kasar dasu toshe shafukan sada zumunta da kuma na sakwanni.

ABNA24 : Wata wasika da hukumar kula da kamfanonin sadarwa na kasar ta fitar ta bukaci da a toshe shafukan ba tare da wata wata ba.

Matakin ya shafi shafukan sada zumunta da suka hada da Facebook,Twitter, WhatsApp, Signal da kuma Viber.

Wannan matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage kwana biyu a je zaben shugabancin kasar, inda za’a fafata tsakanin shugaban kasar, Yoweri

Museveni, da kuma babban abokin hammayarsa, Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine.

342/